in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron FOCAC ya budewa Nijeriya sabuwar kafar samun damarmaki
2018-09-13 09:30:42 cri
Taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, ya yi nasarar gina wani tubali na samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, tsakanin Sin da Afrika, tare kuma da bude sabuwar kafar samun damarmaki ga Nijeriya.

Kakakin shugaban Nijeriya Garba Shehu ne ya bayyana haka, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, inda ya ce taron ya samarwa Nijeriya da ma Afrika baki daya, babbar kafa ta kara fahimta da tabbatar da moriyar juna tsakaninsu da kasar Sin.

Garba Shehu wanda ke cikin jami'ai 20 da suka rako shugaban Nijeriya zuwa taron, ya ce sun koma gida da karin fahimta game da yadda kyakkyawar dangantaka da kasar Sin za ta kasance.

Ya kara da cewa, Nijeriya ta ji dadin damarmakin da taron FOCAC ya gabatar da kuma rattaba hannu kan daftarorin hadin gwiwa, musammam a lokacin da kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afrika ke fama da karancin ababen more rayuwa.

Yayin taron, Shugban kasa Muhammadu Buhari da sauran jami'ansa sun gudanar da taruka da kamfanonin kasar Sin da suka nuna sha'awar zuba jari a bangarori da dama na kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China