Edet Okon, Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, ya ce babu bukatar neman izinin rundunar kafin duba wadanda suka yi hatsari ko suka ji rauni sanadiyyar harbin bindiga.
Sanarwar da kakakin ya fitar a jiya, ta ce rundunar na son gyara wannan kuskure da ake yi, dake hana bada kulawa ga wanda ya yi hatsari ko ya samu rauni daga harbin bindiga, idan babu shaidar izinin rundunar.
A cewarsa, bisa darajar da take ba ran bil adama, rundunar 'yan sandan ta na kira ga dukkan asibitoci da cibiyoyin lafiya, su rika karbar irin wadancan marasa lafiya don gaggauta ba su kulawa da nufin ceton rayuka.
Sai dai ya ce, yayin da ake ba su kulawa, dole ne a gaggauta kai rahoto ga 'yan sanda domin gudanar da bincike da daukar matakan da suka dace. (Fa'iza Mustapha)