in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nijeriya sun fattaki mayakan Boko Haram a Arewa maso gabashin Nijeriya
2018-09-02 16:50:22 cri
Sojojin Nijeriya sun kashe mayakan Boko Haram da dama tare da kwato makamai a yankin Guzamala dake arewa maso gabashin jihar Borno, a wani bata kashi da suka yi a baya-bayan nan.

Sanarwar da kakakin rundunar Col Onyeama Nwachukwu ya fitar, ta ce mayakan bataliya ta 2 ne suka yi bata kashi da 'yan tada kayar bayan.

Nwachukwu ya ce 'yan tada kayar bayan na tada fitina da karban kudi daga hannun mutane, sai dai sun fuskanci tirjiya daga dakarun Operation lafiya dole wadanda suka samu taimako daga takwarorinsu na sama.

Rahotanni sun ce akalla sojoji 30 ne mayakan Boko Haram suka kashe a ranar yayin bata kashin, sai dai kakakin rundunar sojin bai yi bayani dangane da rahoton ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China