in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rushewar wani gini ya yi sanadin mutuwar mutum 1 a Nijeriya
2018-08-18 16:12:09 cri
Wani gini mai hawa 4 ya rufta jiya Juma'a a Abuja babban birnin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda yayin da wasu 18 ke makale karkashin baraguzai.

Kawo yanzu mutane 6 aka ceto, yayin da ake ci gaba da aikin don binciko wadanda suka makale.

Akalla mutane 25 ne ke cikin ginin wanda ake ginawa a unguwar Jabi na Abuja a lokacin da ya rufta jiya da rana.

Mamakon ruwan sama da aka yi a birnin jiya, ya kawo tsaiko ga aikin ceton.

Tuni dai aka fara gudanar da bincike don tantance musababbin rushewar ginin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China