A wani muhimmin jawabin da ya gabatar a helkwatar MDD Guterres ya ce "matukar ba mu sauya tsarinmu ba nan da shekarar 2020, za mu iya rasa alkiblar da za mu bi wajen gujewa matsalar sauyin yanayi, bisa ga irin mummunan sakamako da illolin da yake haifarwa ga bil adama da dukkan al'amurra da suka shafi tsarin muhallin halittu wadanda suke iya ba mu kariya". Ban da haka, Guterres ya bayyana illolin dake tattare da sauyin yanayi ga al'ummomi masu zuwa a nan gaba.
Ya kara da cewa, kamata ya yi a yi amfani da shekara mai zuwa wajen zartas da hukunci game da gudanar da sauye sauye, a matakai na majalisar zartaswar gwanatoci da majalisun dokokin na dukkan kasashen duniya. Ya kamata a bude ido sosai, a gina tsarin gamayya kuma a tabbatar da ganin shugabannin sun saurari batun da kunnen basira.
Babban jami'in ya yi alkawarin yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a taron muhawara na MDD wanda za'a gudanar a ranar 25 ga watan Satumba.
Tuni jami'in ya riga ya tsara taron koli kan batun sauyin yanayi a watan Satumbar 2019. (Ahmad Fagam)