Kakakin majalisar Stephane Dujarric, ya ce kasashe 42, ciki har da wadanda suka fi ba majalisaar gudunmowar 'yan sanda da sojoji, da mambobin kwamitin sulhu ne suka amince da yarjejeniyar aiki tare na taimakawa ayyukan wanzar da zaman lafiya na majalisar.
Ya kuma godewa dukkan kasashen da suka sanya hannu kan daftarin, yana mai cewa, Sakatare Janar Antonio Guterres, na kira ga dukkan mambobin mjalisar, su rattaba hannu kan daftarin kafin ranar 14 ga watan Satumba, gabanin taron manyan jami'ai kan tsarin ayyukan wanzar da zaman lafiya da za a yi ranar 25 ga watan na Satumba.
Taron zai bayyana rawar da MDD ta taka a baya, da kuma wadda take yi a yanzu ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da bayyana kalubalen da take fuskanta da kuma taimakawa wajen inganta shigar sauran kasashen duniya cikin aikin. (Fa'iza Mustapha)