'Yan rakiyar Shugaba Xi sun hada da Ding Xuexiang, mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma mamba a sakatariyar kwamitin tsakiya na jam'iyyar da Darakta Janar na ofishin kwamitin tsakiya na JKS Yang Jiechi, da mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma mamba a majalisar gudanarwar kasar, kana Ministan harkokin waje wato Wang Yi, da kuma mataimakin shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na al'ummar kasar Sin kuma shugaban hukumar rayawa da sake fasalin kasar wato He Lifeng. (Fa'iza Mustapha)