Shugaba Xi wanda kuma shi ne Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne yayin wani taron kasa da ya gudana yau Litinin domin ranar Malamai ta kasar Sin karo na 34.
Ya ce a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar, ya na mika sakon gaisuwa da taya murna ga malamai a fadin kasar.
Ya kuma jadadda bukatar daukaka kwarewa da darajar malamai ta yadda za su mori matsayinsu a cikin al'umma da kuma kara bada gudunmuwa ga maradun jam'iyyar da jama'a, ta hanyar ilmantar da su. (Fa'iza Msutapha)