A sakonsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, a cikin shekaru 70 da kafuwar kasar Koriya ta Arewa, jama'ar kasar sun samu nasarori da dama kan sha'anin raya ra'ayin gurguzu da raya kasa.
Xi Jinping ya jaddada cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar Sin suna dora muhimmanci sosai kan dangantakar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninta da kasar Koriya ta Arewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar kiyayewa da zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A shekarar bana, shugaba Xi ya gana da Kim Jong Un har sau karo uku, sun tabbatar da makomar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shugaba Xi yana son yin kokari tare da Kim Jong Un wajen sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata don amfanawa kasashen biyu da jama'arsu gaba daya da kuma samun zaman lafiya da na karko a yankin. (Zainab)