Wasikar ta ruwaito shugaba Xi na cewa, cikin sama da shekaru 20, taron baje kolin ya zama dandalin inganata zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen duniya da wallafa muhimman bayanai tare da tattauna batutuwan zuba jari.
Shugaba Xi ya kara da cewa, yayin da take cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin za ta ci gaba da kara fadada bude kofarta.
Ya ce ya na fatan taron mai taken inganta zuba jari tsakanin Sin da kasashen duniya, zai iya zama taron kwararru na kasa da kasa da zai zama dandalin sabon zagayen bude kofa da kuma taka muhimmiyar rawa wajen samar da sabbin hanyoyin bude kofa ta kowacce fuska da kuma gina tattalin arzikin duniya a bayyane.
Baje kolin zai fara ne daga yau Asabar zuwa ranar 11 ga wata. (Fa'iza Mustapha)