in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Somalia ta gaggauta amincewa da dokar bada kariya ga masu bukata ta musamman
2018-09-11 10:14:14 cri
Wakilin MDD dake kasar Somalia a jiya Litinin ya bukaci gwamnati da ta hanzarta amincewa da yarjejeniyar kasa da kasa game da bada kariya da kare hakkin mutane masu bukata ta musamman.

Michael Keating, wakilin musamman na sakatare janar a Somalia, ya jaddada cewa mutanen Somali masu bukata ta musamman wani bangare ne mai matukar muhimmanci a cikin al'umma, don haka akwai bukatar a shigar da su cikin harkokin siyasa, da yanayin zamantakewa da harkokin tattalin arzikin kasar.

Keating ya fada cikin wata sanarwa a Mogadishu cewa, Somaliya ta amince da sanya hannu kan yarjejeniyar, don haka mataki na gaba da ya rage shi ne neman amincewar majalisar dokokin kasar.

Dokar ta kasance yarjejeniya ce ta kasa da kasa wadda ta tanadi kare hakkin mutane masu fama da lalurar nakasa. Musamman kasashen da suka amince da yarjejeniyar dole ne su tabbatar da ba da kariya da cikakkiyar dama ga nakasassu domin su amfana daga dukkan hakkoki da 'yanci da sauran mutane ke samu, kuma a martaba su da kare kimarsu a tsakanin al'umma. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China