Wata sanarwar hadin gwiwa da MDD, da kungiyoyin EU, da AU, da ta raya gabashin Afirka ta IGAD, da kuma Amurka da ma wasu sauran kasashe suka fitar, ta yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta, a kuma koma teburin shawarwari.
Sanarwar na zuwa ne, biyowa bayan barkewa tashin hankali a ranar Alhamis, inda sassan biyu suka yi amfani da manyan makamai domin kaiwa juna hari.
Mahukuntan yankunan biyu, sun zargi juna da fara tada rikicin da ya tada hankulan al'umma a yankin na arewacin Somalia. (Saminu Alhassan)