in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somalia: An kaddamar da kafar wayar da kan matasa game da kaucewa shiga kungiyoyin ta'adanci
2018-01-11 10:39:05 cri

Mahukuntan kasar Somalia, sun kaddamar da wata kafa ta yanar gizo wadda za ta taimaka wa matasan kasar kaucewa shiga kungiyoyin ta'addanci, da na masu tsattsauran ra'ayi, a wani mataki na yaki da sauya tunanin 'yan kasar musamman ma matasa.

Da yake kaddamar da kafar a ranar Laraba, ministan ma'aikatar watsa labarai, al'adu da yawon bude ido na kasar Abdirahman Omar Osman, ya ce kafar wadda za ta kasance cikin jerin kafofin sada zumunta da ake amfani da su a kasar, za ta kasance mai tasirin gaske wajen wanzar da zaman lafiya da lumana a Somalia.

Mr. Osman ya kara da cewa, kafar za ta rika samar da bayanai na gaskiya ga matasa, game da alfanun dake tattare da tsarin dimokuradiyya. Za kuma ta raba matasan da duk wata kafa da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ke bi na jirkita tunaninsu.

A daya hannun kuma, hakan zai dakile yunkurin da kungiyar Al-Shabaab ke yi a ko da yaushe, na gurbata tunanin matasan kasar, ta hanyar bayyana aika aikar da kungiyar ke aiwatarwa.

Jami'in ya kara da cewa, sashen na musayar bayanai, zai baiwa matasa damar fito da basirarsu, wadda za ta agazawa ginin kasarsu, da gina kishin kasa da hadin kai a zukatan daukacin al'ummar kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China