in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan AU da MDD na nazarin yanayin tsaro a Somalia gabanin janye dakarun wanzar da zaman lafiya
2017-11-18 13:31:59 cri
Wakilan MDD da Tarayyar Afrika AU, sun kaddamar da wani aikin ziyara domin nazarin yanayin tsaro a fadin kasar Somalia dake kahon Afrika, gabanin janye sojojin wanzar da zaman lafiya cikin shekara mai zuwa.

Shiryen-shiryen wanzar da zaman lafiya na MDD da AU a Somalia sun bayyana a jiya cewa, wakilin musammam na shugaban hukumar AU a Somalia Francisco Caetano Madeira da wakilin musammam na Sakatare Janar na MDD Micheal Keating, sun bi wani ayari domin kai ziyara Barawe, muhimmin birnin dake yankin Lower Shabelle a ranar Alhamis.

Ayarin karkashin jagorancin Firaministan kasar Hassan Ali Khaire, sun gana da shugabannin al'umma da sauran jama'a, game da yuwar mika ragamar tsaron Barawe da a yanzu haka ke karkashin kariyar dakarun shirin wanzar da zaman lafiya na AMISOM ga dakarun Gwamnatin Somalia.

Wata sanarwar da shirin wanzar da zaman lafiya na AU ya fitar, ta ce an kai ziyarar ne a yayin da ake ci gaba da tattauna batun janye dakarun AU daga manyan garuruwan dake yankunan kudanci da tsakiyar kasar, tsakanin Gwamnati da dakarunta da kuma AMISOM.

Ana sa ran dakarun na AU za su mika ragamar tsaron manyan garuruwa ga dakarun Somalia, domin ba su damar jagorantar aikin wanzar da zaman lafiya, kafin janyewar sojojin wanzar da zaman lafiya kamar yadda aka tsara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China