Shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika AMISOM, ya ce ya fara yi wa 'yan bangar Darwish na Jihar Jubbaland rajista, kafin a shigar da su cikin rundunar tsaron yankin.
Shugaban 'yan sandan AMISOM a yankin Kismayo, Martin Abili ya ce sama da 'yan banga 5,000 ne aka yi wa rajista a yankunan Gedo da Lower Juba da kuma Middle Juba.
Wata sanarwa da Martin Abili ya fitar a Mogadishu, ta ce matakin ya dace da shirin AMISOM da na MDD dake da nufin shigar da 'yan bangar cikin rundunar 'yan sanda a Jubbaland, wadanda za a dorawa nauyin tabbatar da doka da oda da kuma tsaro a jihar.
Ya ce rajistan ya kunshi karbar bayanan ko wane mutum, ciki har da hoto da hoton yatsar hannu.
Ya ce za a sanya 'yan bangar cikin rundunar 'yan sandan Jubbaland ko wasu hukumomi tsaro ko kuma rundunar sojin Somalia. (Fa'iza Mustapha)