in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin na ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau, in ji IMF
2018-07-27 11:14:17 cri
Jiya Alhamis, Asusun ba da lamuni na IMF ya kira taron manema labarai a birnin Washington na kasar Amurka, bayan shawarwarin da ya yi tare da wakilan kasar Sin karo na hudu a shekarar 2018, inda ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau.

Asusun na IMF ya yi bayani cewa, kasar Sin ta samu ci gaba a wasu muhimman fannoni, sakamakon kwaskwarimar da ta yi a cikin gida. Kuma gyare-gyaren da ta yi kan ayyukan sa ido ya taimaka wajen rage kabubaloli ta fuskar sha'anin kudi. Sa'an nan, ta ci gaba da rage samar da kayayyakin da suka zarta bukatun a'umma, da kuma inganta ayyukan kare muhalli, da gaggauta ayyukan bude kofa ga waje.

Haka kuma, ya ce, kasar Sin tana cikin lokaci mai muhimmanci, cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta yi ta samun karuwar tattalin arziki da sauri, a halin yanzu kuma, ta fara mai da hankali kan ingancin kayayyaki. Kana, yadda take aiwatar da wannan sauyi, zai taimaka matuka ga bunkasuwar kasar Sin baki daya cikin shekaru da dama masu zuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China