in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya yi kira da a gudanar da aikin fadakar da jama'a yadda ya kamata
2018-08-22 22:14:31 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada muhimmancin gudanar da aikin fadakar da jama'a game da manufofin kasar bisa sabon yanayin da ake ciki yadda ya kamata.

Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kwamitin rundunar askarawar kasar, ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron fadakar da jama'a da aikin yada akidu na kasa da ya gudana ranar Talata a birnin Beijing,fadar mulkin kasar Sin.

Shugaba Xi ya kuma yi kira da a gudanar da aikin fadakar da jama'a game da manufofin kasa ta yadda za a hada kan al'umma a kokarin ganin sun rungumi manufofi da akidu da kyawawan dabi'u, ta yadda za su ba da babbar gudummawa ga yanayin da jam'iyya da ma kasa baki daya ke ciki.

Xi ya ce shawarwari da tsare-tsaren da kwamitin koli na JKS ya yanke tun a babban taron wakilan jama'a na kasa karo na 18 a shekarar 2012 suna bisa turba kuma jami'an dake aikin fadakar da jama'a game da akidu sun dace.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China