in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban jamhuriyar Congo yana son koyi da fasahohin bude kofa da yin kwaskwarima da aka samu a birnin Shanghai na kasar Sin
2018-09-09 16:22:18 cri
Shugaban jamhuriyyar Congo Denis Sassou-Nguesso ya kai ziyara a birnin Shanghai na kasar Sin jiya Asabar, inda ya gana da memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na birnin Shanghai Li Qiang.

A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, shugaban kasar jamhuriyyar Congo ya kai ziyara a kasar Sin, da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC, da kuma yin shawarwari tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta hakan an inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu.

Li Qiang ya kara da cewa, birnin Shanghai yana son yin kokari tare da jamhuriyyar Congo wajen aiwatar da manyan ayyuka 8 da shugaba Xi Jinping ya gabatar a gun taron koli na Beijing na dandalin FOCAC, da kuma ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, da yin amfani da fifikonsu da kara yin hadin gwiwa, da more fasahohi, da rike damar samun ci gaba, ta hakan za a samar da gudummawa wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, shugaba Sassou-Nguesso ya nuna yabo wajen gudanar da taron kolin Beijing na dandalin FOCAC cikin nasara tare da manyan ayyuka 8 da shugaba Xi Jinping ya gabatar a gun taron. Yana son koyi da fasahohin bude kofa da yin kwaskwarima da aka samu a birnin Shanghai, da kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da kuma sa kaimi ga samun babban ci gaba a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China