in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban hukumar WHO a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo dake fama da barkewar cutar Ebola ya kara jefa shi cikin damuwa
2018-08-15 09:52:16 cri
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ya kara shiga damuwa game da sabuwar barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, bayan ziyarar da ya kai kasar a baya-bayan nan.

Yayin wani taron manema labarai a Geneva, Tedros Ghebreyesus, ya ce rikicin da ake ci gaba da yi a arewacin lardin Kivu na kasar, inda aka samu barkewar cutar na kwana nan, ya ba cutar damar samun yaduwa ba tare da tarnki ba.

Ya ce suna kira ga bangarorin masu rikici da su tsagaita bude wuta saboda kwayar cutar barazana ce ga lafiyar kowa, domin ba ta zabar wanda za ta kama.

Kasancewar yankin dauke da wurare da dama masu hatsarin zuwa saboda rikici, inda kuma cutar Ebola ta samu mazauni, da cunkoson jama'a da yawan zirga-zirga a yankin da ke da 'yan gudun hijira sama da miliyan guda, babban kalubale ne ga hukumar WHO da abokan huldarta wajen kai kayayyakin agaji da ake bukata cikin gaggawa.

Kawo yanzu, cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 41, sannan an tabbatar da mutane 30 cikin 75 da ake zargin sun kamu da ita, cikinsu har da ma'aikatan lafiya 7 da wasu 27 da ake kyautata zaton sun kamu.

Tedros Ghebreyesus ya kuma yi kira da a kara tsaurara matakan yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China