Kididdigar wanda hukumar Uganda Debt Network (UDN), tare da hadin gwiwar hukumar kula da kasafin kudi ta kasa da kasa wato (IBP) suka gudanar, ta baiwa kasar ta Uganda maki 60 bisa 100, inda ya zarce kashi 42 bisa 100 wato matsayi na kasa a bisa kididdar ta duniya.
Rahoton ya ce, Uganda ta wallafa 7 daga cikin muhimman takardun kasafin kudin kasar 8, inda ta sanar da jama'ar kasar a lokaci bayan lokaci, inda wannan matakin ya ba ta damar yin fice cikin jerin takwarorinta, musamman kasashen kudu da hamadar saharar Afrika.
Hakan kuma ya baiwa kasar ta Ugandan damar zama a sahun gaba cikin jerin kasashen duniya dake baiwa 'yan kasarsu damar shiga a dama da su wajen tsara kasafin kudin kasar, wato da kashi 28 bisa 100, da matsakaicin matsayi na kashi 12 bisa 100 a duniya.(Ahmad Fagam)