Korar ta biyo bayan rahotannin da kafafen yada labarai suka bayar, na rashin kyawun alakar aiki saboda neman iko da ya kai ga karuwar kashe-kashe da rashin tsaro a kasar dake gabashin Afrika.
Cikin sama da watanni 6 da suka gabata, an kashe akalla mata 26 a birnin Kamfala da tsakiyar lardin Wakiso, kuma har yanzu ba a kama galibin wadanda ke da hannu wajen aikata laifin ba. (Fa'iza Mustapha)