in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi tsokaci kan shawarar "Ziri daya da Hanya daya"
2018-08-27 19:19:28 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron cika shekaru 5 da aka kira a birnin Beijing don tunawa da fara gabatar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya"

A jawabin da ya gabatar shugaban na kasar Sin, ya bayyana cewa shawarar "Ziri daya da Hanya daya" ta dace da bukatar daidaita tsare-tsaren kula da harkokin duniya, da nuna ra'ayi na yin hadin gwiwa don fuskantar kalubale tare, gami da tabbatar da kare hakkin kowa da sauke nauyin dake bisa wuyan kowa.

Shugaban ya jaddada cewa, kamata ya yi, a tsaya kan matakan musayar ra'ayi da tattaunawa, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna, ta yadda kasashen da ke cikin shawarar za su kara imani da juna, da karfafa hadewar tattalin arzikinsu, da musayar al'adu, ta yadda hakan zai haifar da alfanu ga jama'ar kasashen, da kokarin samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin duniya.

A cikin shekaru 5 da suka wuce, shawarar "Ziri daya da Hanya daya" ta kara samun karbuwa a duniya. Kawo yanzu, akwai kimanin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 103 da suka kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa 118 tare da kasar Sin karkashin tsarin shawarar "Ziri daya da Hanya daya".(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China