in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da takwaransa na Iraki sun aikawa juna sakon murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashensu
2018-08-25 15:21:00 cri

Yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na jamhuriyar kasar Iraki Fuad Masum, suka aikawa juna sakwanni domin murnar cika shekaru 60, da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasar Sin da kasar ta Iraki.

Cikin sakonsa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, yana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakanin kasarsa da kasar ta Iraki, kuma yana fatan zai yi kokari tare da shugaba Masum, domin kara karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashensu, a karkashin laimar shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda al'ummar kasashen biyu za su ci babbar gajiya daga shawarar.

Shugaba Masum shi ma ya bayyana a cikin na sa sakon cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin kasashen biyu, ta samu ci gaba lami lafiya, haka kuma sassan biyu sun samu babban ci gaba wajen hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, yana mai fatan kasarsa da kasar Sin za su kara kyautata huldar dake tsakaninsu, domin amfanin al'ummun sassan biyu, tare kuma da ingiza kwanciyar hankali da zaman lafiya da ci gaba a kasashen biyu.

A dai wannan rana, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na Iraki Haider al-Abadi, su ma sun aikawa juna sakwanni, domin murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashensu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China