Shugaban na Amurka wanda ya sanar da hakan ga manema labarai a fadar White House yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Portugal Marcelo Rebelo de Sousa dake ziyara a kasar ta Amurka, ya kuma bayyana cewa, tattaunwarsa da Putin za ta mayar da hankali kan kasashen Syria da kuma Ukraine.
Tun a jiya ne dai fadar Kremlin ta sanar da cewa, ana saran Putin da Trump za su gana a wata kasa. Kuma a yau Alhamis ne za a sanar da rana da kuma wuri a hukumance da shugabannin biyu za su gana.
Wadannan kalamai na zuwa ne, bayan ga shugaba Putin ya yi wata ganawar sirri da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Amurka John Bolton a Moscow. (Ibrahim)