A watan Disamban shekarar 2015 ne aka tsaida kudurin kafa cibiyar hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kiyaye muhalli a wajen taron kolin dandalin FOCAC a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Kafa irin wannan cibiya muhimmin mataki ne da aka dauka wajen tabbatar da aiwatar da wasu manyan shirye-shirye goma na inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka. Kana, Sin za ta aiwatar da wasu ayyuka 100 na samar da makamashi mai tsabta da na neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a nahiyar Afirka.
A dayan bangaren kuma, kokarin da kasar Sin take yi wajen kiyaye muhalli ya samu amincewa da yabo daga kasashen duniya. Inda mataimakiyar darektar zartaswa ta hukumar kiyaye muhalli ta MDD, Madam Joyce Msuya ta ce, kasar Sin ta yi kwaskwarima a fannin kiyaye muhalli, da son koyawa sauran kasashe nasarorin da ta samu a wannan fanni. Joyce ta ce, karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin muhalli zai amfanawa jama'ar Afirka baki daya.(Murtala Zhang)