Jami'ai da malamai da kwararru daga kasashe daban-daban na Afrika, na ganin ba makawa, Afrika za ta mayar da RMB matsayin takardar kudin ajiya na ketare da kuma kudin da ake cinikayya da shi a nan gaba, wannan ba bunkasa tattalin arzikin kasar kadai zai yi ba, har ma da karawa takardar kudin karfin samun karbuwa a duniya.
Rahotanni na cewa, kasashe kamar Rwanda, sun sanya RMB cikin takardar kudin ketare da suke ajiya da ita. Sannan kasashen Afrika ta kudu da Nijeriya da wasu kasashe, sun sanya hannu kan yarjejeniyar musayar takardar kudi da kasar Sin, yayin da Kenya da Zimbabwe da Botswana suka nuna sha'awarsu ta fara amfani da ita a matsayin takardar kudin ajiya. (Fa'iza Mustapha)