in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda: Mutane 3 sun jikkata a yayin wani harbi a London
2018-08-21 10:56:33 cri
A kwai mutane 3 ne aka raunata a yayin harbe harbe a daren ranar Litinin a wajen wata tashar karkashin kasa dake arewacin London, wata sanarwar 'yan sandan yankin ta tabbatar da hakan.

"Jami'anmu suna wajen da aka yi harbe harben a kan titin Kingsbury da misalin karfe 9:45 na dare daidai karfe (2045GMT) agogon GMT a ranar Litinin. Ba shi da alaka da ta'addanci. An kwashe mutane 3 zuwa asibiti, wadanda aka yi ammana ba su da cutarwa," "yan sandan birnin London sun bayyana hakan a cikin shafinsu na Twitter.

Kakakin hukumar 'yan sandan ya ce: "'Yan sanda da motar daukar marasa lafiya na London suna zaune cikin shirin ko-ta-kwana tun da misalin karfe 9:45 a daren Litinin, 20 ga watan Augasta, tun bayan samun rahotannin harbe harben a titin Kingsbury."

'Yan sandan sun ce an rufe titunan sai dai kawo yanzu ba'a kama kowa ba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China