in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mutane 12 dake da alaka da harin birnin London yayin wani samame
2017-06-05 11:09:42 cri

Hedkwatar rundunar 'yan sandan birnin London, ya ce an kama mutane 12 wadanda ke da alaka da harin da aka kai birnin a ranar Asabar da dare, yayin samamen da aka kai gidan daya daga cikin maharan a yankin Barking dake gabashin birnin London.

Har ila yau, rundunar ta ce jami'an tsaro na ci gaba da binciken wasu gidaje a yankin na Barking.

Kafar yada labarai ta Sky News ta ruwaito mutanen dake zaune a rukunin gidaje na Elizabeth Fry dake titin Kings na Barking, inda gidan daya daga cikin maharan yake na cewa, an yi ta harbe-harbe kuma jami'an tsaro dauke da manyan makamai ne suka kai samame da sanyin safiyar jiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China