Saurayin da aka kashe mai suna Edir Frederico Da Costa na da shekaru 25 da haihuwa. A ranar 15 ga watan Yunin da muke ciki ne kuma, 'yan sanda sun tare motarsa a unguwar Newham dake gabashin birnin London, sa'an nan sun ba shi kashi, tare da fesa masa hayaki mai sa hawaye. Daga baya matashin ya rasu kwanaki 6 bayan an kai shi asibiti.
A wajen tarzomar da aka yi a karshen makon da ya gabata, 'yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe wutar da masu zanga-zangar suka kunna da taimakon 'yan sanda.
A cewar jami'an 'yan sandan kasar, ba a kama kowa ba ya zuwa yanzu, sai dai wasu 'yan sanda dake bakin aiki yayin tarzomar sun ji raunuka sakamakon arangamar da ta auku. (Bello Wang)