in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Burtaniya sun bayyana mutane biyu da ake zargi da kai harin gadar Landan
2017-06-06 11:01:59 cri
A ranar Litinin 'yan sandan a Burtaniya suka bayyana mutane biyu daga cikin 'yan ta'adda uku da ake zargi da hannu wajen kitsa harin gadar Landan su ne, Khuram Shazad Butt da Rachid Redouane, kamar yadda kafafen yada labaran cikin gida na kasar suka rawaito.

Butt, mai shekaru 27, wanda dan asalin kasar Pakistan ne, dake zaune a gabashin birnin Landan tare da matarsa da yayansa shekaru masu yawa da suka gabata, kamar yadda BBC ta rawaito. Har ma an ce ya taba shiga cikin wani shiri na tarihi da BBC ta shirya game da tsattsauran ra'ayi mai taken Jahadi shi ne kofa ta gaba wato Jihad is Next Door.

Maharin na biyu shi ne Rachid Redouane, mai shekaru 30, ya bayyana kansa a matsayin dan asalin kasashen Moroccan da Libyan, shi ma yana zaune a wannan yankin na gabashin Landan.

Sky News ya ruwaito jami'an 'yan sandan na cewa, Rachid Redouane an tabbatar cewa ya zauna a kasar Ireland sama da shekara guda tsakanin 2014 da 2016 kuma matarsa 'yar asalin Scotland ce.

Jami'an Scotland sun ce, 'yan sanda suna da masaniya game da Butt tun shekaru biyu da suka gabata, amma ba su da wani bayanan sirri dake nuna cewa yana da alaka da kaddamar da hari.

'Yan sanda sun fitar da hotunan maharan biyu, kuma suna bincike domin tabbatar da ko wadannan mutanen su ne a hakaki. 'Yan sandan sun nemi jama'a da su ba su bayanai game da wadannan mutanen da ake zargi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China