in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara harajin da Amurka za ta sanyawa kayayyakin Sin zai kawo illa ga rayuwar masu sayayya na Amurka
2018-08-21 10:50:29 cri

Jiya Litinin, ofishin wakilan harkokin cinikayya na kasar Amurka ya kira taron jin ra'ayin jama'a kan batun kara harajin kwastam kan hajojin kasar Sin da darajarsu ta kai dallar Amurka biliyan dari 2, inda aka tattauna kan jerin kayayyakin da za a kara sanya musu harajin da suka kama daga kashi 10 bisa dari zuwa kashi 25 bisa dari.

Bisa takardun da kamfanoni da kungiyoyin kasar Amurka suka gabatar a yayin wannan taro, sun nuna cewa, matakin da kasar Amurka ta dauka zai kara kudaden da masu sayayya na kasar Amurka za su kashe a rayuwarsu ta yau da kullum, kuma babu wadda za ta iya maye gurbin kasar Sin a fannin samar da kayayyaki masu inganci da yawa.

Kara harajin kwastam kan hajojin kasar Sin zai haddasa illa ga kamfanonin kasar Amurka, musamman ma kananna da matsakaitan kamfanoni wadanda suke dogaro kan cinikin dake tsakanin kasa da kasa.

Haka kuma, cikin takardar da kungiyar kasuwanci ta kasar Amurka ta bayar, ta nuna cewa, matakin kara harajin kwastam kan hajojin kasar Sin zai bata ran masu sayayya da kamfanonin kasar, har ma da tattalin arzikin kasar baki daya. Don haka, kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin kasar Amurka da kasar Sin da su yi shawarwari yadda ya kamata kan batun cinikin dake tsakanin bangarorin biyu.

Taron da aka bude a jiya Litinin za a shafe kwanakin aiki shida ana yinsa, wakilan kamfanoni da kungiyoyi sama da 350 ne ake sa ran za su halarci wannan taro. A maimakon kara harajin kwastam kan kayayyakin masana'antu da na yanar gizo kamar yadda aka saba yi, jerin kara harajin da aka tsara ya shafi kayayyakin amfanin gida, kujerun jariran da ake sanyawa a cikin motoci, kayayyakin ado da dai sauransu. Rahotanni na nuna cewa, matakin zai kara kudaden da masu sayayya na kasar Amurka za su kashe kan harkokin yau da kullum. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China