in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sukar aboki da wuka a baya, za a iya amincewa da Amurka?
2018-08-13 10:30:42 cri

Yayin da Turkiya ke fuskantar kalubalen raguwar darajar kudinta, Amurka ta ba da umurnin ninka harajin da Turkiya za ta biya, kan karafa da sanholo da za ta fitar zuwa Amurka, wato an buga wa kasar haraji na kaso 50 cikin dari ga karafa, da kaso 20 cikin dari ga sanholo.

Matakin dai ya sa an aza ayar tambaya kan Amurka cewa, ko wane irin mataki za ta dauka kan sauran kasashe? Saboda ta iya jefa aminiyarta cikin mawuyacin hali. Shin ko Amurka za ta ci gaba da kasancewa wata kasa dake daukar sauke nauyin dake wuyanta na kasa da kasa da za a iya amincewa da ita ko a'a?

A hakika dai, ana da irin wannan tambaya tun bayan taron koli na Sicilia na G7 da aka gudanar a bara, inda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta taba bayyana bakin cikinta kan Amurka. Ta ce, Zamanin amincewa da juna tsakaninta da sauran aminai ya kare, kamata ya yi Turawa su dogara da kansu.

Rukunin nazarin zabe na Jamus, wanda ya yi bincike kan ra'ayin jama'a ya ba da wani rahoto a watan Mayu na bana, yana mai cewa Jamusawa kaso 82 cikin dari suna ganin cewa, Amurka ba ta zama wata abokiya da za a iya amincewa da ita ba, yayin da kaso 36 cikin dari suke ganin cewa Rasha ta fi samun amincewarsu.

Ya zuwa yanzu, Turkiya na fuskantar mawuyacin hali, amma tana da sauran hanyar da za ta bi. Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, Turkiya za ta zabi sauran abokai, Alal misali, Iran, Rasha ko sauran kasashen Turai. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China