in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kai karar Amurka domin ta dauki matakai ga kayayyaki masu amfani da hasken rana da ta shigar da su
2018-08-15 10:35:10 cri
Kasar Sin ta kai karar Amurka karkashin tsarin warware rikici na kungiyar WTO, game da matakan kariya da Amurkar ta dauka kan kayayyakin da take samarwa masu amfani da karfin hasken rana da ba da rangwame ga makamashin da za a iya sabuntawa da ake samarwa kasar. A jawabin da ta gabatar a jiya, kakakin ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta ce, matakan Amurka sun kawo illa ga moriyar ciniki ta kasar Sin, a don haka Sin ta kai kara don kare moriyarta da ka'idojin tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban.

Kakakin ta yi nuni da cewa, kafin hakan, Amurka ta dauki matakai kan kayayyaki masu amfani da karfin hasken rana da Sin ta shigar kasar, wato ta kara buga musu harajin kwastam da kashi 30 cikin dari, wanda mataki ne da ya sabawa yarjejeniyar matakan kariya na kungiyar WTO. Yayin da kasar Amurka ta dauki wannan mataki, ta samar da rangwame ga kayayyaki masu amfani da karfin hasken rana da sauran makamashin da za a iya sabuntawa da kasar ta samar da kanta, matakin da ya samar da sauki ga kamfanoninta na samar da makamashi mai tsafta ta hanyar da ba ta dace ba, wanda kuma suka kawo illa ga moriyar kamfanonin Sin a wannan fanni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China