in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin BMW ya zama na farko da ya shan wuya sanadiyyar takaddamar ciniki
2018-08-06 16:15:30 cri
Kamfanin kera motoci na BMW na kasar Jamus, ya daga farashin motocin SUV samfarori biyu da ya fitar zuwa kasar Sin da kashi 4 cikin dari da kuma kashi 7 cikin dari, wadanda ya kera su a kasar Amurka, bisa karuwar yawan kudin da aka kashe wajen sayen kayayyakin kera motocin. Kuma dalilin karuwar yawan kudin da ya kashe shi ne, takaddamar cinikin da Amurka ta tayar na kara kakkabawa sauran kasashe haraji, matakin da ya sa farashin sassan injuna kera motocin BMW da aka kera a Amurka ya karu. A hannu daya kuma, Sin ta kara buga haraji kan motocin da ta shigo daga kasashen waje kirar Amurka da kashi 25 cikin dari, wato gaba daya ta bugawa wadannan motoci harajin kaso 40 cikin dari daga ranar 6 ga watan Yuli, don mayar da martani. Abin da ya nuna cewa, yawan motoci kirar Amurka da za a sayar a kasuwannin kasar Sin zai ragu saboda hauhawar farashinsu.

Kamfanonin kerar motoci na kasa da kasa ba za su son yin watsi da kasuwar kasar Sin ba, saboda kasuwar tana matsayin farko a duniya wajen sayen motoci a cikin shekaru 9 masu zuwa. Kamfonin BWM da Benz sun ce, idan Amurka ta ci gaba da tada zaune tsaye, ta yadda za su yi illa su rage motocin da za su kera a kasar tare da sallamar wasu ma'aikatansu na kasar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China