in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Rasha: Rasha za ta mayar da martani kan sabon takunkumin da Amurka za ta yi mata
2018-08-21 09:40:07 cri
A jiya Litinin, sakataren watsa labaru na shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya ce, Rasha za ta mayar da martani kan sabon takunkumin da kasar Amurka za ta kakaba mata da sunan kare muradun kasarta.

Kamfanin dillancin labaru na Rasha TASS ya ruwaito Peskov na cewa, fadar Kremlin ta fahimci cewa, Amurka na shirin daukar sabon matakin kakabawa kasar Rasha takunkumi, kuma Rasha ta gano cewa, matakin da Amurka za ta dauka aiki ne na "rashin zumunci da keta dokar kasa da kasa", kuma hakan na iya kawo illa ga harkokin cinikayyar kasa da kasa.

Yayin da yake tabo batun takunkumin da mai yiwuwa Amurka za ta kakaba wa masu ayyukan shimfida bututun gas na Nord Stream 2, Peskov ya bayyana cewa, aikin Nord Stream 2 aiki ne da ya shafi cinikayyar kasa da kasa, kuma matakin Amurka na adawa da aikin ya saba wa dokokin cinikayya.

Peskov ya kara da cewa, shugaban kasar Rasha Valadmir Putin ya bayyana cewa, yana kokari ganin an samu ci gaban dangantaka a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, da kawar da tashin hankalin dake faruwa tsakanin kasashen biyu.
Baya ga haka, Peskov ya bayyana cewa, sakataren tsaron Rasha Nikolai Patrushev da mai ba da taimako ga shugaban kasar kan harkokin tsaron kasa na Amurka John Bolton za su gana a 'yan kwanaki masu zuwa a Geneva, inda za su tattauna kan wasu muhimman batutuwan na kasa da kasa.  (Bilkisu)
 
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China