Kituyi ya ce, a 'yan shekarun nan, harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afirka sun shiga wani sabon mataki karkashin tsaron dandalin FOCAC. Kuma kafa yankin cinikayya maras shinge da aka yi a birnin Shanghai, ya kafa wani sabon dandamali wajen shigo da kayayyakin Afirka kasar Sin, da cike gibin cinikayya dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, abun da ya sa ingancin cinikayyar bangarorin biyu ke kara kyautatuwa.
Har wa yau, Kituyi ya ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya fitar na taimakawa ci gaban kasuwancin Sin da Afirka, haka zalika tana taimakawa kasashen Afirka daban-daban wajen raya masana'antunsu.(Murtala Zhang)