in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Tunisiya: Taron FOCAC na Beijing wani sabon mafarin alakar Sin da Afirka
2018-08-13 19:12:52 cri
Jakadan kasar Tunisya dake nan kasar Sin Dhia Khaled ya bayyana cewa, taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) da zai gudana cikin watan Satumban wannan shekara a birnin Beijing na kasar Sin, zai kasance wani sabon mafari da zai kara ciyar da alakar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare zuwa gaba.

Jakada Dhia Khaled wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a nan Beijing, ya bayyana taron a matsayin taro na tarihi, wanda zai kara samar da damammaki da sassan biyu za su kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, da kara samar da ci gaba gami da fahimtar juna.

Bugu da kari, taron zai samar da wata sabuwar makoma ga hadin gwiwar Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya da al'adu,da Ilimi da kimiya da fasahar kere-kere.

Khaled ya bayyana fatan cewa, taron zai taimaka wajen fadada jarin da kasar Sin dake zubawa a Afirka. Ya kuma darajanta ci gaban alakar Sin da Afirka bisa akidar mutunta juna da dangantakar dai-dai wa daida da samun moriya tare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China