in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kasashen Afirka sun lashi takwabin yakar ayyukan ta'addanci a kan iyakokinsu
2018-08-10 09:16:53 cri

A jiya ne kasashen Sudan da Libya da Chadi da Nijar suka amince su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, ta yadda za su yaki kalubalen tsaro da suka hada da ayyukan ta'addanci da sauran manyan laifuffukan da ke faruwa a kan iyakokinsu.

Ministan harkokin wajen kasar Sudan mai masaukin bakin taron ministan kasashen karo na uku Al-Dirdiri Mohamed Ahmed shi ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabin bude taron na birnin Khartoum. Ya kuma bayyana muhimmancin sake kaddamar da cibiyar musayar muhimman bayanai tsakanin kasashen hudu.

Ministan ya ce, nasarar da dakarun kasashen Sudan da Chadi suka samu na tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen biyu, ya nuna irin nasarar da aikin hadin gwiwar zai haifar.

A nasa jawabin, ministan tsaron Jamhuriyar Nijar Kalla Mountari, ya yi kira da a hanzarta tsara matakan hadin gwiwar tabbatar da tsaron kan iyakokin kasashen, musamman ta hanyar bullo da dabarun musayar muhimman bayanai kan tsaron iyaka, duba da irin kalubalen da kasashen yankin ke fuskanta.

A watan Yunin da ya gabata ne kasashen hudu suka sanya hannu kan wata yarjejeniya a birnin N'Djamenan kasar Chadi, game da yadda za a tabbatar da tsaro da sa-ido a kan iyakokin kasashen.

Yarjejeniyar ta amince a rika yin sintiri na hadin gwiwa a kan iyakokin kasashen, da musayar muhimman bayanai, da kafa cibiyar ayyukan hadin gwiwa da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa a kan iyakokin kasashen hudu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China