in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin tsaro a yankin yammacin Afrika sun lashi takobin aiki tare don magance laifukan da ake aikatawa a kan iyakoki
2017-06-21 09:35:24 cri

Shugabannin hukumomin tsaro na kasashen yankin yammacin Afrika, sun yanke shawarar yin aiki tare domin magance laifukan da ake aikatawa a iyakokin yankin.

Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya Ibrahim Kpotum Idris, ya shaidawa manema labarai a wajen taron yini biyu kan tsaro na kasashen yankin yammacin Afrika dake gudana a Accra na kasar Ghana cewa, ta hanyar hadin gwiwa ne kadai za a iya magance laifukan.

Ibrahim Idris ya kuma ambato batun kame Chikudu Evans da jami'an tsaro suka yi a farko wannan watan, wanda ya kasance bata gari da ya yi kaurin suna, inda yake zaune da iyalinsa a Ghana amma ya ke aikata laifukansa a Nijeriya.

A cewarsa, Chikudu da ake zargi da satar mutane ya mallaki fasfo guda biyu, daya na Nijeriya, dayan kuma na kasar Ghana, a don haka akwai bukatar hada hannu wajen karewa da magance irin wadannan laifukan.

Taron ya samu halartar shugabannin rundunonin 'yan sanda, da na hukumomin kula da shige da fice, da masu tsaron iyakoki, da na hana fasa kauri, da 'yan sanda masu tsaron teku, da kuma jami'an kamfanoni masu baje kolin kayayyakin samar da tsaro na zamani.

A nasa bangare, babban sufeton 'yan sandan Ghana David Asante-Apeatu cewa ya yi, tun da laifuka sun fara tsallakawa kasashen waje, dole ne a hada hannu wajen daukar matakai da za su tabbatar da tsaron yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China