Ministocin tsaron Afirka dake taro a birnin Kampalan kasar Uganda, sun amince su kafa wata rundunar kota-kwana, wadda za a rika tura ta ko'ina a fadin nahiyar a duk lokacin da aka samu rahoton barkewar tashin hankali.
Ministocin dai na wannan taro ne karkashin wani shiri na kara karfin nahiyar ta hanyar kafa rundunar kota-kwana (ACIRC), shirin da aka kafa a watan Nuwanban shekarar 2013 da nufin daukar matakan soja a duk lokacin da wani tashin hankali ya barke a nahiyar.
Bugu da kari, ministocin da kuma wakilan gwamnatoci daga kasashen Aljeriya, da Angola, da Burkina-Faso, da Chadi, da Masar, da Rwanda, da Senegal, da Tanzaniya, da Afirka ta kudu, da Nijar, da Sudan, da kuma Uganda mai masaukin baki, sun yanke shawarar gabatar da shawarwarin da aka cimma a wannan taro ga shugabannin kasashensu a yayin taro na gaba don neman amincewarsu.
A jawabinsa kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro Smail Chergui, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, da su ba da gudummawa ga asusun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar, ta yadda rundunar ta ACIRC za ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Daga karshe ministocin sun amince su gana a watan Oktoban wannan shekara, inda ake fatan za a tsara kudaden tafiyar da rundunar da irin ayyukan da za ta gudanar, tsarin samun gargadi daga jami'an kungiyar da kuma alkawuran da ko wace kasa ta yi.
Ita dai wannan runduna za ta kasance ta wucin gadi ne kafin rundunar nahiyar ta din-din-din (ASF) da ake fatan kafawa a shekarar 2018. (Ibrahim)