An gudanar da dandalin zaman lafiyar kasashen duniya karo na 5 a nan birnin Beijing tsakanin ranar 16 zuwa 17 ga wata, yayin dandalin ne kuma aka shirya wani taro kan "hadin gwiwar tsaron Afirka", wanda ya samu halartar ma'aikatan diflomasiyya da tsoffin 'yan siyasa da masanan da abin ya shafa daga kasar Sin da wasu kasashen Afirka da dama, inda suka tattauna kalubalen da kasashen Afirka ke fuskanta a halin yanzu, da bullo da matakan hadin gwiwa a fannin tsaro tsakanin Sin da Afirka da dai sauransu.
Masanan da ke halartan taron sun yi nuni da cewa, kasashen Afirka suna fatan za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin, bisa dalilin cewa, shawarar da kasar Sin ta gabatar game da shirin nan na "ziri daya da hanya daya" da kuma wasu matakan da kasar Sin ta dauka kan kasashen Afirka sun sha banban da matakan da Turawan mulkin mallaka da kasashen Turai a yanzu suka dauka.
Jakadar kasar Afirka ta Kudu madam Dolana Msimang ta bayyana cewa, ta amince da cewa, a karkashin tsarin "ziri daya da hanya daya", Sin da Afirka suna iya kyautata yanayin tsaron Afirka ta hanyar yin hadin gwiwa tsakaninsu, saboda kara karfafa cudanyar tattalin arziki shi ma zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare kuma da taimakawa kasashen da abin ya shafa samun ci gaba. Shugaban cibiyar nazari kan manufofin Afirka da ke kasar Kenya Peter Kagwanja ya yi nuni da cewa, kasar Sin ba da ta makarkashiyar mamaye Afirka, wannan ya sha banban da manufar wasu kasashen ta samun moriya a nahiyar.(Jamila)