in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afirka da su magance matsalar cin hanci da halatta kudin haram don inganta makomar nahiyar
2018-08-09 09:15:57 cri

Babbar sakatariyar hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arzikin Afirka (ECA) Vera Songwe ta ce, muddin kasashen nahiyar Afirka suna son inganta makomar nahiyar, har ma al'ummunsu su kasance masu samun matsakaicin kudin shiga, to wajibi ne su magance matsalolin cin hanci da halatatta kudin haram da kin biyan haraji.

Alkaluman hukumar ta ECA na nuna cewa, a cikin shekaru 30 da suka gabata har zuwa shekarar 2009, nahiyar ta yi hasarar a kalla dalar Amurka triliyan 1.4, baya ga wasu kudaden da suke sulalewa na hanyoyin da ba su shafi harkokin kasuwanci ba da suka kai dala biliyan 27 a ko wace shekara tsakanin shekarar 2005 zuwa 2014.

Nahiyar Afirka dai karkashin inuwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, na daukar wannan batu da muhimmancin gaske, har ma ta kafa wata tawaga mai karfi karkashin jagorancin tsohon shugaban Afirka ta kudu Thabo Mbeki, inda suke tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kokarin ganin an dakile makudaden kudaden da suke sulalewa daga nahiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China