in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Kudu da hamadar Sahara ne ya fi fama da safarar haramtattun kudade
2016-06-12 12:50:25 cri

Mashawarci ga tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Mojanku Gumbi, ya ce, mai yiwuwa ne yawan kudaden da ake fitarwa a ko wace shekara daga nahiyar Afirka ta barauniyar hanya, ya kai kusan dalar Amurka biliyan 90.

Mr. Gumbi ya ce, darajar wadannan kudade ya kai ribi daya da rabi, na yawan daukacin kudaden da kasashen ketare ke baiwa nahiyar a matsayin kudaden tallafi a duk shekara.

Ya ce, wadannan kudade dake zurarewa daga Afirka, sun kunshi wadanda ake samu bayan aikata laifuka daban daban, da na masu kaucewa haraji, da kuma kudaden dake da alaka da laifukan cin hanci da rashawa.

Jami'in ya ce, hanyoyin da suka dace a bi wajen shawo kan wannan matsala sun hada da kafa wani tsari na ko-ta-kwana, wanda zai maida hankali ga yaki da masu yiwa tattalin arzikin nahiyar ta'annati.

Kaza lika a cewar sa, akwai bukatar sanar da al'umma bayanai game da dukiyoyi, da kadarori da ake boyewa a kasashen ketare. Kana bankuna su rika tantance dukkanin mamallaka asusun ajiyar kudade da ake kai musu, domin kaucewa amfani da bankunan wajen boye kudaden haram.

Gumbi ya bayyana hakan ne gabanin taron wakilan majalissun dokokin kasashen nahiyar Afirka, da kasashen Caribbean, da na yankin tekun Pacific, da kasashen dake kungiyar tarayyar Turai, taron da za a bude a ranar Litinin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China