in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kasashen Afirka da su fito da sabbin hanyoyin tara kudaden shiga da za su gudanar da ayyukan raya kasa
2016-07-22 11:31:53 cri

MDD ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su fito da sabbin hanyoyin samun kudaden shiga wadanda za su gudanar da ayyukan raya kasa, maimakon dogaro da tallafi daga kasashen ketare.

Wani rahoto da aka fitar a gefen taron kula da harkokin cinikayya na MDD (UNCTAD) da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ya bukaci gwamnatocin kasashen na Afirka, da su dauki kwararan matakai da kuma hana karuwar basussukan da ake binsu ta yadda za su zama matsala ga kasashe nasu, kamar yadda aka gani a shekaru 30 da suka gabata.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, daga shekarar 2006 zuwa 2009, babu kasa a Afirka da bashin da ake bin ta bai kai karu zuwa kaso 7.8 cikin 100 a shekara ba. Adadin da rahoton ya ce, daga shekarar 2011 zuwa 2013 ya karu zuwa kaso 10 cikin 100 a shekara. Wato kimanin dala biliyan 43 ko kuma kaso 22 cikin 100 na kudaden shiga da kasar da ta samu a shekarar 2013.

Babban sakataren dandalin na MDD Mukhisa Kituyi ya bayyana cewa, galibin kasashen Afirka sun fara kirkiro sabbin hanyoyin samun kudaden da aiwatar da manufofin ci gaba mai dorewa, maimakkon dogara kan tallafin kasashen katare da suka saba yi a baya.

A saboda haka, rahoton ya bukaci kasashen Afirka da su yi tunanin wasu hanyoyin samun kudaden shiga ta yadda za su inganta rayuwar al'ummominsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China