in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano halin cin amanar Amurka kan rigingimun cinikayya
2018-08-01 19:31:28 cri

Kawo yanzu rigingimun cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka na ci gaba har tsawon watanni hudu da wani abu, yanzu kuma rigingimun sun gamu da wata sabuwar matsala.

Wani rahoton da kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya fitar, ya nuna cewa, sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin yana yin shawarwari a asirce da wakilin mataimakin firayin ministan kasar Sin Liu He domin sake gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, a sa'i daya kuma, kila Amurka za ta fara kara sanya haraji kan kayayyakin kasar da za a shigar Amurka, wadanda darajarsu za ta kai dalar Amurka kusan biliyan 16 tun daga yau 1 ga watan Agusta, kana an yi hasashe cewa, gwamnatin kasar Amurka tana shirin kara haraji kan kayayyakin da za ta shigo daga kasar Sin, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200 kimanin kaso 25 bisa dari, amma a baya ta sanar da cewa, za ta kara harajin kaso 10 bisa dari.

Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa, tana son yin shawarwari da gwamnatin kasar Sin kan batun, amma a sa'i daya, tana daukan matakin kara harajin kan kayayyakin kasar Sin, wannan ya nuna cewa, ba ta nuna magana guda a kan lamarin, sai dai tana son kara samun riba daga wajen ne kawai, hakika gwamnatin kasar Sin ba ta yi mamaki ba, saboda kafin wannan, gwamnatin Amurka ta sha cin amana, a don haka gwamnatin kasar Sin a shirye take domin mayar da martani kan matakan cin amanarta.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China