in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta bukaci a gaggauta kwashe bakin haure daga kasarta
2018-07-06 10:39:42 cri
Ministan harkokin wajen gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD Mohamed Sayala, ya bukaci a gaggaunta kwashe bakin haure dake kasar Libyan don sake mayar da su kasashensu na asali.

Sayala ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da William Swing, babban daraktan hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM), a Tripoli, inda jami'an biyu suka tattauna game da kokarin da ake na dakile ayyukan bakin haure, kamar yadda gidan talabijin na Libyan ya rawaito.

Sayala ya fada a taron manema labarai na hadin gwiwa da mista Swing cewa, dole ne su kara kokari wajen kwashe bakin haure don sake mayar dasu kasashensu da kuma rage wa'adin da ake dauka wajen tsugunar da bakin hauren a kasar, wanda ya dace da manufofin hukumomin kasar ta Libya.

Darakta janar na IOM ya yabawa kokarin da hukumomin Libyan ke yi wajen cetowa da kuma bada matsuguni ga bakin hauren da kuma kokarin da suke wajen sake mayar da bakin hauren kasashensu na asali.

Dakarun tsaron tekun kasar Libya sun ceto dubban bakin haure a tekun kasar tun a watannin farkon wannan shekara ta 2018.

A bisa alkaluman hukumar IOM, kimanin bakin haure 9,000 ne aka mayar dasu kasashen su a watanni shidan farko na wannan shekarar ta 2018. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China