in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kasashen Afirka da su bullo da dokokin da za su bunkasa cinikayya ta yanar gizo
2018-07-24 09:54:11 cri

MDD ta bukaci kasashen Afirka da su bullo da managartan dokokin da za su taimaka wajen bunkasa harkokin cinikayya ta yanar gizo.

Babban sakataren taron MDD kan harkokin cinikayya da raya kasashe(UNCTAD) Mukhisa Kituyi shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin taron harkokin cinikayya ta yanar gizo da kungiyar AU ta shirya a birnin Nairobin kasar Kenya. Ya ce rashin kyakkyawan yanayi da tsari, ya sa nahiyar zama kurar baya cikin takwarorinta na duniya a fannin cinikayyar yanar gizo.

A don haka ya ce akwai bukatar kasashen na Afirka su bullo da managartan dokoki da za su karfafa samar da cibiyoyin cinikayyar yanar gizo, wadanda za su samu amincewar masu saye da sayarwa.

Jami'in ya ce, tsarin cinikayyar yanar gizo na kunshe da tarin damammaki fiye da tsohon tsarin cinikayya, duba da yadda tsarin zai baiwa kananan masu samar da kayayyaki damar shiga kasuwannin duniya.

Kituyi ya ce, ya zuwa karshen shekarar 2017 kasashen Kenya da Afirka ta kudu da Najeriya wadanda suka kasance a sahun gaba a wannan fanni, sun gudanar da harkokin cinikkaya ta yanar gizo na a kalla kaso 6 cikin 100 .

Manufar taron na yini uku dai ita ce samar da wata dama ta kara fahimtar yadda cinikayya ta yanar gizo ke gudana a nahiyar Afirka, da kalubale da damammaki dake kunshe cikin tsarin, da yadda za a dora kan ci gaban da aka samu a halin yanzu a nahiyar, gami da sauran yankunan duniya. Haka kuma taron zai tattauna muhimman fannonin da za a bunkasa fasahohin na'urori masu sarrafa kansu a nahiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China