in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen ketare sun jinjinawa wasan kwaikwayon gargajiyar Sin
2018-07-31 10:27:39 cri

Wasan Inuwar Piying mai salon yankin Sanxia, wani irin wasan kwaikwayon gargajiya ne da ake gudanarwa a garin Wushan dake birnin Chongqing, da kuma wasu wuraren dake kewayansa. Wasan wanda ya samo asali daga fasahar yanka takarda, yana nuna al'adu da tarihin yankin Sanxia kwarai da gaske.

A ranar 30 ga wata, tawagar 'yan jaridu ta zirin tattalin arzikin kogin Yangtse, ta kai ziyara dakin baje koli na Wushan dake birnin Chongqing, inda suka kalli wasan inuwar Piying mai salon yankin Sanxia, wasan da ya samu yabo daga 'yan jaridu na kasashen ketare kwarai da gaske. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China