Sabon hasashen bankin duniya ya nuna ci gaba tattalin arzikin duniya cikin shekaru biyu masu zuwa na nan kamar yadda hasashen baya ya nuna, sai dai ya yi gargadin yiwuwar samun mataloli, ciki har da karuwar matakan tsaurara cinikayya.
A sabon rahoton da ya fitar jiya game da ci gaban tattalin arzikin duniya, bankin ya ce, tattalin arzikin duniya zai karu da kaso 3.1 a bana, kafin ya sauka zuwa kaso 3 a badi, kamar da yadda aka yi hasashe a watan Janairun bana.
Ana sa ran tattalin arzikin kasashen da suka ci gaba zai dan tsagaita da kaso 2.2 a bana, inda zai sauka zuwa kaso 2 a shekara mai zuwa, yayin da manyan bankuna ke rage kudin da suka zuba don bunkasa tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)