Kudurin mai lamba 2431, wanda ya samu amincewar daukacin mambobin kwamitin 15, ya kuma yanke shawarar rage yawan jami'an shirin na AU da ake kira AMISOM masu kayan sarki zuwa 20,626 ya zuwa watan Fabrerun badi, da kuma 'yan sanda 1,040 a matsayin adadi mafi karanci.
Sabon kudurin ya biyo bayan makamancinsa da aka amince da shi ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata, wanda ya tsawaita wa'adin aikin AMISOM zuwa yau, 31 ga wata, a wani nazari na kwararru, domin bada damar tantance ayyukan shirin bisa hadin gwiwar MDD da AU.
Kudurin na watan Mayu ya yi hasashen rage jami'an AMISOM masu kayan sarki zuwa 20,626 ya zuwa ranar 30 ga watan Oktoban bana. (Fa'iza Mustapha)